Tambayoyin Auratayya: 01
Вставка
- Опубліковано 30 лис 2024
- Wannan Sabon Shiri ne da Babban Malaminmu @amdaurawa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah) Ya fara gabatarwa a Ranar 6-Rabi'ul Awwal wanda yayi dai-dai da 02/October/2022. Inda Malamin namu yake amsa tambayoyin da suka shafi auratayya kadai. Ga masu son aiko da nasu tambayoyin sai su tura su zuwa ga akwatun Sakonmu Kamar Haka auratayya101@gmail.com.
Ga Tambayoyin Kamar Haka:
1.Assalamualaikum malam fatan mun tashi lfy, Allah ya sa hakan
Ameen.
Malam mijina ne yake da matsala, idan ya kusance ni ko yazo inda
nake gaba daya sai yayi ta korafi nan na ciwo can naciwo ko Kuma
cikin dare ya tashi yana ta ihu da firgici, malam a haka har ta kai ga
abun inya tashi yayi ta fada yace shi bazai iya ba ya sakeni, a haka
yanzu anyi saki uku, yanzu ya dawo wai yaje an mishi fatawa cewa ba
a cikin hankalinsa yayi ba aure na nan. Malam wannan fatawa da aka
bashi Tana da inganci ko Bata da asali ?
2. Aslm Allah ya qara wa malam lfy da nisan kwana malam shin
yamastayin Wanda yayi Wasa da mace ana azume har azuminsa
yakarye daga bayan azuminsa yakarye yasadu da matar malam Allah
ya qara fasaha
3. Assalamu alaikum akaramakallah ni ina cikin damuwa sosai akwai
wata yarinya da nake so zan aura mun dade muna soyayya to kuma
lokaci guda sai na fara fuskantar wasu abubuwan daga gareta karshe
ma dai yanzu ban kiranta bata kira na na kasa cireta a raina kullum
tunata nakeyi shine nake so a banj shawara yaza,I na manta da ita a
rayuwa ta.?
4.Assalamu alaikum akaramakallah ni ina cikin damuwa sosai akwai
wata yarinya da nake so zan aura mun dade muna soyayya to kuma
lokaci guda sai na fara fuskantar wasu abubuwan daga gareta karshe
ma dai yanzu ban kiranta bata kira na na kasa cireta a raina kullum
tunata nakeyi shine nake so a banj shawara yaza,I na manta da ita a
rayuwa ta
4. Malam muna maka fatan alkhairy Allah ya kara lafiya da nisan
kwana. Malam shekararmu uku kenan da aure amma mijina baya kula
da wasu daga cikin hakkokina, yana bani ci da sha da sutura amma
daga wannan to bani da maraba da roommate a wajensa. Ina mishi
duk wani abu da nasan ze dawo da hankalinshi wurina amma
ni kadai ke kidi na nake rawa ta. Nayi mashi magana ba
sau daya ba ba biyu ba akan hakan yana sa inji yana fita a raina amma
baya saurarana malam har sai da takai gaba daya naji bana sonshi
kuma baya burgeni duk abunda yayi har nakan fada masa maganganu
marasa dadi wani lokacin. Da ya fahimci haka yanzu malam sai yake
kokarin gyarawa amma wlh ko kadan hakan baya burgeni kuma
banajin shi a raina saboda hakan. Shin malam akwai laifi in na nemi
ya sallameni? Saboda Ina gudun na cigaba da Saba mashi Ina Saba
ma ubangiji na. Malam ku bani shawara. Nagode
5. Assalamu Alaikum
Malam Barka da warhaka,Yaya kokari,Allah Ya azurtaku da
Ikhlaasi, Allah Yasa Aljannah ce Makoma Ameen.
Malam shin Ya halatta miji ya tilastawa Matarsa Qayyade
haihuwa (kamar yace yara uku yakeso ta Haifa? sa’annan menene
hukuncinsa na kaurace mata tsawon wata biyar a dalilin kin
Amincewarta akan hakan.?