Sana'o'i biyar nake yi domin ciyar da iyalaina - Matashi mai Diploma | Legit TV Hausa

Поділитися
Вставка
  • Опубліковано 23 сер 2024
  • Sana'o'i biyar nake yi domin ciyar da iyalaina - Matashi mai Diploma | Legit TV Hausa
    Matasa da yawa kan kasance cikin wani irin hali musamman bayan sun kammala karatu amma aikin gwamnati ya gagara, ga kuma iyali da aka fara tarawa. Hakan kan tilasta masu zuciya daga cikinsu fantsama cikin sana'o'in dogaro da kai domin ganin cewa sun rufawa kansu da iyalansu asiri.
    Daga cikin ire iren wadannan matasan, Legit TV Hausa ta ci karo da wani matashi a jihar Bauchi mai suna Abubakar A.K.A, wanda ya labarta yadda yake yin sana'o'i biyar a lokaci daya, domin ganin ya ciyar da iyalansa, duk da cewa ya yi karatu har zuwa matakin Diploma, amma rashin aikin gwamnati da kuma rashin damar ci gaba da karatun ya sa dole ya fantsama yin sana 10 maganin mai gasa.
    A cikin labarin Abubakar A.K.A Bauchi, akwai darasi mai tarin yawa da al'umma za su koya, musamman matasan da suka kammala karatu, amma suka dage lallai sai sun samu aikin gwamnati ba tare da tunanin fara sana'o'i domin dogaro da kawunansu ba.

КОМЕНТАРІ • 3

  • @sulemanaishat4248
    @sulemanaishat4248 4 роки тому

    Allah ya taimakemu

  • @LegitTVHausa
    @LegitTVHausa  4 роки тому

    Sana'o'i biyar nake yi domin ciyar da iyalaina - Matashi mai Diploma | Legit TV Hausa

  • @lordkarma672
    @lordkarma672 4 роки тому

    You change legit tv news to Funani .very very poor