Najeriya ta ciyo bashin tiriliyan 101… • RFI Hausa

Поділитися
Вставка
  • Опубліковано 1 жов 2024
  • Bayanai na nuni da cewar jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 101, biyo bayan ƙarin rancen kusan dala biliyan 5 da gwamnatin ƙasar ta karɓa daga Bankin Duniya kaɗai a bara.
    A shekerar ta 2023 dai, ofishin kula da basukan Najeriya ya ce ya zuwa watan Disambar da ya gabata yawan bashin da ake bin ƙasar ya kai naira Tiriliyan 97. Lamarin da ya sanya masana bayyana damuwa kan yawan kuɗaɗen ruwan da ƙasar za ta riƙa biya kkna rancen da ta yi.
    Kan haka muka tattauna da Dakta Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki a jami’ar Kashere da ke jihar Gombe a Najeriyar.

КОМЕНТАРІ •