Rikici da Makomar Masarautar Kano - (Muhammadu Sanusi II Vs. Aminu Ado Bayero)

Поділитися
Вставка
  • Опубліковано 21 сер 2024
  • Babu shakka siyasa na da matukar tasiri ga sarautun gargajiya a wannan zamani da muke ciki.
    Rikicin Masarautar Kano Tsakani Sabon Sarki Sanusi Lamido Sanusi wanda aka sani da Muhammadu Sanusi da kuma tsohon Sarki Aminu Ado Bayero :
    Tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake nada Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 bayan shekaru huɗu da tuɓe shi ake cigaba da dambarwa kan wannan lamari.
    A ranar Juma'a ne dai aka miƙa wa Sarki Sanusi II shaidar komawa karagar masarautar Kano a matsayin sarki na 16 a jerin sarakunan Fulani, kamar yadda BBC Hausa suka rawaito a shafin su na internet.
    A shekarar 2020 ne dai gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiro ƙarin sabbin masarautu huɗu sannan daga bisani aka tumɓuke Muhammadu Sanusi II daga karagar Sarkin Kano.
    Sai dai ana cikin wannan bato sai ga sarki Aminu Ado shima ya shigo kano, inda a wannan rahoto na Muryar Amurka suka fayyace lamarin.

КОМЕНТАРІ •