Ban san garau-garau ba, ko "Pure Water" bana sha sai ruwan roba - G-Fresh Al'ameen

Поділитися
Вставка
  • Опубліковано 3 жов 2024
  • Mawakin nan G-Fresh Al'ameen da ke tashe a kafafen sada zumunta ya ce, shi bai san wata garau-garau ba, domin ko Pure Water baya sha.
    G-Fresh ya bayyana hakan ne lokacin da yake martani ga masu ganin baikensa har suke masa bidiyo idan yana al'amuransa ba tare da ya sani ba.
    A zantawarsa da Jamila Galadanci a Dala FM ya bayyana yadda ya tsinci kansa a duniyar waka, har ma da yadda ya rikiɗe yake tallan CD dinsa da kansa.

КОМЕНТАРІ • 64