BASHIR HALILU TV
BASHIR HALILU TV
  • 82
  • 131 818
ALJANU MASU JIKIN WUTA DA TARIHIN MASARAUTARSU
JINNUN NARIY
جن الناري
Aljanin Wuta.
Daga Shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Su Jinnun Nariy ko kuma Jinnun Nariyyuwna a jam'i, su ne mafiya muhimmanci a cikin tarihin nau'ukan Aljanu saboda dalilai guda biyu.
Na farko dai su ne asalin Aljanu kafin samuwar kowane irin nau'in Aljani saboda Allah Ya halicci tsatson Aljanu ne daga wuta.
.
Iblis shi ne Kakan Aljanu kuma Allah ya halicce shi ne daga harshen wuta, shi da kuma sauran 'ya'yansa da mabiyansa.
Daga baya ne aka samu wasu nau'ukan Aljanu ta dalilin rarraba wajen zamansu da abincinsu da kuma yanayin halittar jikinsu.
Daga cikin nau'ukan Aljanu daɗaɗɗu a duniya wadanda su suka fara samuwa daga Jinnun Nariy akwai Jinnul Ghauwas, wanda wasu suke kira Jinnul Ma'iy, saboda suna zama a cikin ruwa. Shafin Bashir Halilu ya jima da kawo cikakken bayani akansu.
Sannan akwai Jinnul Banna'i ko kuma Jinnut Turabiy wato Aljanu Magina kokuma Mazauna cikin kasa.
Kasancewar Aljanu sun rarraba wajen zamansu, wasu suna zaune a cikin kogi, wasu a cikin sahara, wasu a kan bishiyoyi, shi yasa aka samu rabe-raben Aljanu amma asalinsu dai Jinnun Nariy ne.
Haka nan aqida ta qara rarraba Aljanu, inda aka samu masu bautar wuta da masu bautar rana da masu bautar kakaninsu da dai sauransu. Inda wasu kuma suka kasance musulmai.
Rarrabuwar Aljanu zuwa nau'i-nau'i har ila yau, yana da alaqa da launin halittarsu; domin wasu farare ne, wasu baqaqe, wasu jajaye dadai sauransu.
Hatta kasancewarsu masu fika-fiki da marasa fuka-fuki, da masu manyan halitta wadanda sun fi mutane girma da kuma masu kananan halitta wadanda basu fi girman tururuwa ba, ya kara sabbaba rarrabuwar Aljanu zuwa jinsi-jinsi da nau'i-nau'i.
Malamai suka ce : Aljanu sun fara kasuwa zuwa kabila goma sha biyu ne daga 'ya'yan Iblisa La'anahUllah, sannan daga baya kowace kabila ta cigaba da rarrabuwa.
.
Daga cikin Qabilun farko akwai qabilar Ifriytu da Jinnul Mariyd wadanda dukkansu Jinnun Nariyyuna ne wato Aljanu masu jikin wuta.
Dalili na biyu da yasa Jinnun Nariy suke da Muhimmanci a tarihin Aljanu shi ne mafi yawan Ayoyin Alqur'ani da Hadisai suna magana ne akan cewa an halicci Aljanu ne daga wuta, su kuma sune suke da alaqa ta kai tsaye da wuta a yanayin jikinsu. Sukan iya hura wuta da bakinsu ko su kunna gobara.
Kusan kashi saba'in bisa dari na Jinnun Nariy Shaiɗanu ne masu bin tafarkin Iblis. Yawancin Musulman Aljanu ana samunsu ne a wasu jinsunan daban.
YADDA HALITTAR JINNUN NARIY TA KE.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700,08134434846.
Wannan nau'in Aljanu basu da wata dauwamammiyar halitta da suke akanta, kasancewar Allah Ya halicce su da ga6o6i mabambanta yadda Ya so, musulmansu da kafuransu.
Misali wajen idanunsu da hannuwansu da kafafunsu. Akwai mai ido biyu, akwai mai ido arba'in, akwai mai ido daya tak; wani kuma idanuwansa suna tsakanin haka ko sama da haka. To haka ma halittar sauran jikinsu take.
Domin akwai mai hannuwa da yawa wani kafafuwansa ne da yawa da dai sauransu.
Jinnun Nariy Sunay wa sauran Aljanu fariya da cewa su ne asalin Aljanu kuma suna da karfi sosai da taurin kai a fagen yaqi.
Jinnun Nariy kamar mafi yawa daga sauran nau'in Aljanu, suna iya canjawa daga wata halittar zuwa wata kuma suna da saurin canjawa da 6acewa. Ba kamar Tabriyqul Jinni ba wadanda basa iya canja halitta kuma basa saurin 6acewa mutane.
Jinnun Nariy suna cikin Aljanu masu dadewa a duniya amma dai rayuwarsu bata wuce shekara dubu daya da dari biyu duk da dai ana samun Aljani mai shekaru dubu goma sha biyu. Ba a maganar Jinnut Tabaddul wadanda ake ganin kamar mutuwa ta mance da su, wasu masanan ma sun ce basa mutuwa amma dai shafin Bashir Halilu ya taɓa kawo cikakken bayani akansu.
Ayoyin Alqur'ani da yawa sun bayyana cewa an halicci Aljanu ne da wuta. Mun yi bayanin wannan tuni lokacin da muke bayani aka ASALIN HALITTAR ALJANU amma dai ga Hadisi guda daya za mu kawo yanzu.
.
ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ - ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ - ﻋﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ﻗﺎﻝ : ﺧﻠﻘﺖ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻣﻦ ﻧﻮﺭ ، ﻭﺧﻠﻖ ﺍﻟﺠﺎﻥ ﻣﻦ ﻣﺎﺭﺝ ﻣﻦ ﻧﺎﺭ ، ﻭﺧﻠﻖ ﺁﺩﻡ ﻣﻤﺎ ﻭﺻﻒ ﻟﻜﻢ " . ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
.
.
Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
yace " An halicci Mala'iku ne daga haske, an halicci Aljanu daga harshen wuta kuma an halicci Annabi Adam daga abinda akay muku bayani". (wato ta6o).
YADDA MUTUM ZAI GANE JINNUN NARIY YA SHIGA JIKINSA KO KUMA YA SHAFE SHI DA CUTA.
DA
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
★Yawan mafarkin gobara
★Mutum zai dinga mafarkin ya fada wuta ko kuma wuta tana bin sa a guje.
★Mutum zai dinga yawan yin gobara a duk inda ya ajjiye kayansa.
★Zafin kirji da zafin tafin kafafuwa.
★Jan ido da tashin jijiyoyin wuya.
Da dai sauransu.
Daga Shafin Bashir Halilu, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci dana gargajiya. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Переглядів: 538

Відео

TARIHIN MASARAUTUN ALJANU DA DUNIYOYINSU
Переглядів 192Рік тому
TARIHIN MASARAUTUN ALJANU DA DUNIYOYINSU. Daga littafin Jagoran Mai Ruƙiyyah. Aljanu na daga cikin Bayin Allah Maɗaukakin Sarki waɗanda Ya halitta domin su bauta maSa, kamar yadda Allah Ta'a ya ce: { وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ } Aljanu na daga cikin halittu ɓoyayyu da Allah Maɗaukakin Sarki ya halicce su daga wuta, tun kafin Ya halicci mutane, sannan su ne abokan z...
MAGANIN ƘARFIN MAZA NA GARGAJIYA. Sabon binciken...
Переглядів 73Рік тому
Sabon binciken da aka yi akan maganin kara kuzarin maza wajen kusantar iyali. Binciken haɗin magungunan ya haɗada yadda maganin ke magance yawancin cututtukan mata masu alaƙa da sanyin mara.
DR. BASHIR MAI MAGANIN ISLAMIC MEDICINE DA NA GARGAJIYA. LAMBAR WAYAR MALLAM +2348162600700.
Переглядів 118Рік тому
DR. BASHIR MAI MAGANIN ISLAMIC MEDICINE DA NA GARGAJIYA. LAMBAR WAYAR MALLAM 2348162600700. @BBCHausaOfficial #maganin #mata #hausa #musulunci #kano
YAJI DAKAN MAZA DA KUMA YAJI HADIN MATA
Переглядів 605Рік тому
YAJI DAKAN MAZA DA KUMA YAJI HADIN MATA
ILLOLIN MASTURBATION GUDA 21
Переглядів 152Рік тому
ILLOLIN MASTURBATION GUDA 21
WANNAN BUDURWAR MALAMINTA NE YA SA TA SHIGA BANDAKI BA TAKALMI TA YI WANKE SHI NE ALJANU SU KA
Переглядів 216Рік тому
WANNAN BUDURWAR MALAMINTA NE YA SA TA SHIGA BANDAKI BA TAKALMI TA YI WANKE SHI NE ALJANU SU KA
Wadannan Aljanu sun shiga jikin yarinyar ne a lokacin da ta ke wanke a bandaki
Переглядів 3602 роки тому
Yadda wadansu Aljanu su biyu su ka shiga jikin yarinya yar makaranta lokacin da aka saka ta wanki bandaki a makarantarsu. #addu'o'i #how #magunguna #shawarwari #fatawowi #cututtuka #sihiri #asiri #rukiyya #ruq'yah #aljanu #Bashir #halilu #08162600700 #tarbiyyah #islamiyyah #sunnah #medicine #albishir #islamic #green #screen #jinns #demons #aliens #emulates #haunted #ghost #devil #demonology #an...
JAGORAN MAI RUKIYYAH WAJEN KAMA ALJANI DA KONA SHI
Переглядів 1,2 тис.2 роки тому
JAGORAN MAI RUQIYYA Abubuwan da ke cikin littafin. 1-MENENE ALJANI? b) Wa aka fara halitta, mutum ko Aljan? c) Da me aka halicci Aljanu? d) Shin Aljanu Yayan Iblis ne? e) Guraren zaman Aljanu f)Abincin Aljanu g) Addinin Aljanu h) Acikin Aljanu akwai mutanen kirki akwai na banza. Akwai wawaye akwai masu hankali. i) shin Aljanu sun san gaibu? 2) RABE-RABEN ALJANU a)Jinnut Tayyar ﺟﻦ ﺍﻟﻄﻴﺎﺭ Wato Al...
AMFANIN WASU TSIRRAI GUDA 29 WADANDA IDAN KA SANSU ZA KA IYA MAGANCE KOWACE IRIN CUTA KASHI NA (1)
Переглядів 2822 роки тому
AMFANIN WASU TSIRRAI GUDA 29 WADANDA IDAN KA SANSU ZA KA IYA MAGANCE KOWACE IRIN CUTA KASHI NA (1)
ALAMOMIN CIWON ZUCIYA DA MAGANCE SHI
Переглядів 3 тис.2 роки тому
ALAMOMIN CIWON ZUCIYA DA MAGANCE SHI
MAGANIN FIBROID WATO TSIRON MAHAIFA
Переглядів 1722 роки тому
MAGANIN FIBROID WATO TSIRON MAHAIFA
Yadda mu ka yi da Aljani Michael. Shekararsa goma sha ajikin yarinyar
Переглядів 8532 роки тому
Wannan Aljani ya ce ya shafe sama da shekaru goma ajikin wannan yarinya, yana cutar da ita. Ya bayyana adadin yawansu ajikinta da sunayensu. Allah Yay mana tsari daga sharrinsu, Amiyn. Daga shafin Mallam Bashir Halilu. Lambar wayar Mallam 08162600700, 08134434846. #addu'o'i #how #magunguna #shawarwari #fatawowi #cututtuka #sihiri #asiri #rukiyya #ruq'yah #aljanu #Bashir #halilu #08162600700 #ta...
Karawarmu da Aljani Shaddadu
Переглядів 3732 роки тому
Yadda mu ka kara da Aljani Shaddadu. Hatsabibin Aljani mai taurin kai amma daga baya ya musulunta. Daga Mallam Bashir Halilu. Lambar wayar Mallam 08162600700. #addu'o'i #how #magunguna #shawarwari #fatawowi #cututtuka #sihiri #asiri #rukiyya #ruq'yah #aljanu #Bashir #halilu #08162600700 #tarbiyyah #islamiyyah #sunnah #medicine #albishir #islamic #green #screen #jinns #demons #aliens #emulates #...
Saurari Aljanin da bakinsa ya ce tun tana shekara bakwai ya shiga jikinta, yanzu kuma shekararta 20
Переглядів 3682 роки тому
A yayyin gabatar da wannan rukiyyah, Aljanin ya yi bayani dabakinsa cewa tun yarinyar tana karama ya shiga jikinta, wai tafiyarta ce ta ke burge shi. Kuma ya turo ma ta Aljanu kala-kala irinsu Dangaladima don su taya shi aiki akanta amma duk sun kasa. #musulunci #rukyah #addini #mallam #yadda_ake #jinn #aljanu #maganin #magungunan #bashir #08162600700 #hausa #kano
Yadda ake hada magungunan da ke kina Aljani da kashe shi ta hanya mai sauki
Переглядів 1,8 тис.2 роки тому
Yadda ake hada magungunan da ke kina Aljani da kashe shi ta hanya mai sauki
Waliyyai daga jinsin Aljanu. Acikin Aljanu akwai Waliyyayi, mutanen kirki: Mallam Bashir Halilu.
Переглядів 7202 роки тому
Waliyyai daga jinsin Aljanu. Acikin Aljanu akwai Waliyyayi, mutanen kirki: Mallam Bashir Halilu.
Bayanin nau'o'in Aljanu 25 tare da hotunansu. In kana jin tsoro kar ka kalla. Sunnah Medicine
Переглядів 2 тис.2 роки тому
Bayanin nau'o'in Aljanu 25 tare da hotunansu. In kana jin tsoro kar ka kalla. Sunnah Medicine
QUR'AN: SURATU T-H
Переглядів 402 роки тому
QUR'AN: SURATU T-H
SURATU MARYAM: QUR'AN
Переглядів 402 роки тому
SURATU MARYAM: QUR'AN
QUR'AN: SURATUL KAHF
Переглядів 412 роки тому
QUR'AN: SURATUL KAHF
HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MUSULUNCI.
Переглядів 1452 роки тому
HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MUSULUNCI.
MATSAYIN KAMBUN IDO A ADDININ MUSULUNCI
Переглядів 992 роки тому
MATSAYIN KAMBUN IDO A ADDININ MUSULUNCI
Matsayin aiki da Aljanu da neman taimakonsu a addinin Musulunci.
Переглядів 3742 роки тому
Matsayin aiki da Aljanu da neman taimakonsu a addinin Musulunci.
AMFANIN DABINO WAJEN KYAUTATA LAFIYA. HEALTH BENEFITS OF DATE FRUITS
Переглядів 4712 роки тому
AMFANIN DABINO WAJEN KYAUTATA LAFIYA. HEALTH BENEFITS OF DATE FRUITS
Introduction in the Ghost kingdom house.
Переглядів 1092 роки тому
Introduction in the Ghost kingdom house.
AN KAMA SU SUN SAKA LAYA A KABARI ACIKIN MAKABARTA. SUN JE ZIYARAR KABARIN MAHAIFIYARSU.
Переглядів 2872 роки тому
AN KAMA SU SUN SAKA LAYA A KABARI ACIKIN MAKABARTA. SUN JE ZIYARAR KABARIN MAHAIFIYARSU.
Introduction.
Переглядів 512 роки тому
Introduction.
YADDA YAN DAMFARA SU KA KIRA WANI DAN BOKON ABUJA A WAYA. AI KUWA YA YI MAGANINSU.
Переглядів 3702 роки тому
YADDA YAN DAMFARA SU KA KIRA WANI DAN BOKON ABUJA A WAYA. AI KUWA YA YI MAGANINSU.
YADDA ZA KA AZABTAR DA ALJANI BA TARE DA KA SHA WAHALA BA. Bashir Halilu +2348162600700.
Переглядів 5612 роки тому
YADDA ZA KA AZABTAR DA ALJANI BA TARE DA KA SHA WAHALA BA. Bashir Halilu 2348162600700.

КОМЕНТАРІ